Babel

Hasumiyar Babila/The Tower of Babel (Genesis 11: 1-9)

هَوُسَ / Yaren Hausa (Hausa)

  1. A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.
  2. Sa'ad da mutane suke ta yin ƙaura daga gabas, sai suka sami fili a ƙasar Shinar, suka zauna a can.
  3. Sai suka ce wa juna, "Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai." Suka yi aiki da tubali maimakon dutse, katsi kuma maimakon lāka.
  4. Sai suka ce, "Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna, domin kada mu warwatsu ko'ina bisa duniya."
  5. Ubangiji kuwa ya sauko ya ga birnin da hasumiyar da 'yan adam suka gina.
  6. Ubangiji kuwa ya ce, "Ga su, su jama'a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su shawarta su yi da zai gagare su.
  7. Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna."
  8. Haka kuwa daga wurin Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya, sai suka daina gina birnin.
  9. Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya.

Ajami (Arabic) script

Tower of Babel in Hausa in the Ajami (Arabic) script

Source: Farawa (Genesis). Hausa Ajami Transliteration 2004. Niamey, Niger.

Hausa Ajami text contributed by Wolfgang Kuhl

Information about Hausa | Phrases | Numbers | Tower of Babel

Tower of Babel in Chadic languages

Hausa, Mafa, Marba, Massa, Musey, Psikye, South Giziga

Other Tower of Babel translations

By language | By language family

[top]


Green Web Hosting - Kualo

You can support this site by Buying Me A Coffee, and if you like what you see on this page, you can use the buttons below to share it with people you know.

 

SpanishPod101 - learn Spanish for free

If you like this site and find it useful, you can support it by making a donation via PayPal or Patreon, or by contributing in other ways. Omniglot is how I make my living.

 

Note: all links on this site to Amazon.com, Amazon.co.uk and Amazon.fr are affiliate links. This means I earn a commission if you click on any of them and buy something. So by clicking on these links you can help to support this site.

[top]

iVisa.com